An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa

Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da aikatawa, a yanzu an tube shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta

Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da aikatawa, a yanzu an tube shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta ko mukami daga tsohon yariman Birtaniya Andrew, wanda da ne ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II.

Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham Palace ce da kanta ta fitar da sanarwa game da hakan. A yanzu “za a rika kiransa da tsuran sunansa, wato Andrew Mountbatten Windsor,” in ji sanarwar.

Masarautar na fatan wannan mataki nata zai kawo karshen muhawara kan jerin abin kunyar da ake zargin yariman ya aikata wadanda ake alakantawa da masarautar.

Yanzu an tube shi karfi da yaji, duk wasu sarautu da ke kansa, kamar yariman York da sauran su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted