Hare-haren Isra’ila Sun Kashe Mutane fiye da 60 a Gaza

Sama da Falasdinawa 60, ciki har da yara 22 ne suka yi shahada  a jerin hare-haren jiragen yakin  Isra’ila suka kai a wurare da dama

Sama da Falasdinawa 60, ciki har da yara 22 ne suka yi shahada  a jerin hare-haren jiragen yakin  Isra’ila suka kai a wurare da dama a yankin Gaza A cikin sa’oin da suka gabata, A cewar majiyoyin lafiya.

Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a lokaci guda kan gidaje, masallatai, da sansanonin ‘yan gudun hijira. Wakilin Al-Mayadeen ya ruwaito cewa an kai wani harin bam a kan  gidan iyalan Abu Dalal da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, inda aka  kashe mutane 10, ciki har da yara uku. An kuma kai hari gidan iyalan Aql da ke sansanin, wanda ya yi sanadiyyar shahadar  mutane uku da kuma jikkata da dama, yayin da Isra’ila take ci gaba da kai hari ta sama a yankin.

A Deir al-Balah, Falasdinawa uku sun yi shahada  kuma wasu da dama sun jikkata lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari kan sansanonin  mutanen da suka rasa gidajensu a gabashin Asibitin Al-Aqsa, a cewar majiyoyin lafiya na asibiti.

Sojojin mamayar Isra’ila sun kuma kai hari kan gidan iyalan Abu Sharar da ke sansanin ‘yan gudun hijira na al-Bureij, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar.

Bugu da ƙari, mutane da dama sun samu raunuka a wani harin bam da aka kai kan wani tanti da ke ɗauke da mutanen da suka rasa matsuguni a cikin makarantar Abu Hmeisa a wannan sansanin. Asibitin Al-Awda ya tabbatar da karɓar wasu mutane da suka ji rauni sakamakon harin da Isra’ila ta kai wa sansanin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted