Kungiyar Kwallon Kafa Ta Futsal Ta Matan Iran Sun Sami Nasara Akan Kasar Bahrain

Kungiyar kwallon kafa ta “Futsal” ta matan Iran ta zura kwallaye 14-0 a wasan da ya hada ta da takwararta ta kasar Bahrain mai masaukin

Kungiyar kwallon kafa ta “Futsal” ta matan Iran ta zura kwallaye 14-0 a wasan da ya hada ta da takwararta ta kasar Bahrain mai masaukin baki.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka bude wasannin nahiyar Asiya na kwallon kafar Futsal a kasar Bahrain. A wasan farkon, kungiyar ta Iran ta sami nasara akan takwararta ta Hong kong ta hanyar zura kwallaye shida.

Wasa na biyu da Iran din ta yi shi ne da kungiyar kasar Bahrain, da ta sami galaba da kwallaye 14 da 0.

‘Yan wasan na Iran sun kunshi Fatima Shukrani, Niyayash Rahmani, Dhanaz Bakiri, Haidis Yari da kuma Narjis Amir Muhsini.

Ya zuwa yanzu dai kungiyar kwallon Futsal ta Iran tana da maki 6 kuma ita ce a kang aba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted