Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da kawokarshen tattaunawa da kasar Canada dangane da batun kasuwanci
Shugabann a kasar Amurka ya zargi Canada da yin amfani da kalmomin tsohon shugaban kasar Amurka Ronald Regan ta hanayar da ba ta dace ba a cikin wasu tallace-tallace akan kudaden fito, inda ya bayyana cewa; ” Saboda la’akari da halayyarsu an kawo karshen tattaunawar kasuwanci da kasar Canada.”
Shugaban kasar na Amurka ya ci gaba da cewa; Cibiyar Ronald Ragan ta sanar da cewa, Canada ta murguda zancen Regan akan illolin kudin fito, kuma an yi hakan ne domin yin tasiri a cikin matakin da kotun koli ta Amurka za ta dauka akan batun da ake jiran ta fitar da hukunci nan gaba.
Cibiyar ta Regan ta wallafa sako a shafinta na X cewa; hukumar yankin Ontario a kasar Canada ta yanko maganar tsohon shugaban kasar ta Amurka da ya yi a watan Aprilu a 1987, don haka tana tunanin matakan da za ta dauka akan haka ta fuskar shari’a.
A can kasar ta Canada hukumar yankin Ontario ta sanar da cewa, maganar Regan da ta watsa ta jawo hankalin Donald Trump.
Firimiyan gundumar ta Ontario a Canada Dodge Ford ya ce; Na tabbata Trump ba zai ji dadin wannan sanarwar da mu ka wats aba.
Tun da fari, Fira ministan kasar ta Canada Mark Joseph Carney ya fada wa manema labaru cewa; Ba za mu bar Amurka ta cimma manufarta wacce babu adalci a ciki ba dangane da batun kasuwanci.”
Kasar ta Canada dai tana takaddama da Amurka akan batun kara kudaden fito da Trump yake yi kasashe abokan kasuwanci.