Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya

Kungiyar ‘yan wasan kokawar Iran na gargajiya na matasa ‘yan kasa da shekaru 23, ta lashe kambun duniya bayan da ta samu lambobin yabo mafi

Kungiyar ‘yan wasan kokawar Iran na gargajiya na matasa ‘yan kasa da shekaru 23, ta lashe kambun duniya bayan da ta samu lambobin yabo mafi yawa.

Kungiyar ta Iran ta sami lambobin zinariya 3, da azurfa 1 da kuma tagulla 2.

‘yan wasan da Iran da su ka sami kyautar zinariyar sun hada Iman Muhammadi mai ajin nauyi kilio 72, da Gulam Ridha Farakhi mai ajin nauyi kilo 87 da kuma Fardin Hidayati mai ajin nauyi 130.

Wanda ya  sami azurfa kuwa shi ne Sajjad Abbaspur mai ajin nauyi kilo 60, sai kuma wadanda su ka sami tagulla da su ne Ahamd Ridha Muhsin Najad mai ajin nauyi 67,sai Abul Fadal Muhmadim ai ajin nauyi 82.

Kungiyar ta Iran ta zama ta daya da maki143, yayin da kungiyar kasar Ukiraniya ta zama ta biyu da maki 96, sai kasar Azerbaijan da maki 93.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Iran take zama zakara a fagen kokawar gargajiya ba, domin ta zo na daya a shekarun 2022 da 2024. A shekarar 2023 kuwa an hana ‘yan wasan kokawar na Iran izinin shiga kasar Albania ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted