An tsara cewa a cikin wannan makon da aka shiga ne dai za a gana a tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha domin share fagen ganawar shugabannin kasashen biyu.
Fadar mulkin Amurka “ White House” ta bayyana cewa an yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin ministocin harkokin wajen Amurka Marco Rubio da Sergey Lavrov a shekaran jiya inda su ka cimma matsaya akan cewa, ganawar ba ta zama dole ba.
A makon da ya shude ne dai shugabannin kasashen Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladmir Putin su ka yi ttataunawa ta wayar tarho, inda su ka cimma matsaya akan ganawa a birnin Budaphast na kasar Bulgaria.
A cikin watan Ogusta na wannan shekarar an yi ganawa a tsakanin shugabannin Amurka Donald Trump da na Rasha Vladmir Putin a jahar Alaska ta Amurka.