Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda

Rahotanni su bayyana cewa gwamnatin birtaniya ta sanar a hukumance cire kungiyar tahrirush shams HTS daga cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wani yunkuri na

Rahotanni su bayyana cewa gwamnatin birtaniya ta sanar a hukumance cire kungiyar tahrirush shams HTS daga cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wani yunkuri na ganin ta kara kusantar  sabuwar gwamnatin siriya bayan faduwar gwamantin Bashar Al-Asad.

Gwamnatin birtaniya ta bayyana cewa wannan mataki zai sanya su kara kusanci da gwamnatin siriya da Abu mohammad Al-Jolani ke jagoranta wanda aka fi sani da Ahmed sharaa wanda shi ne shugaban kungiyar Al-Qaida kuma kwamandan Daesh.

Wannan sanarwar ta zo ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen birtaniya David lammy ya kai kasar siriya  a watan yuli, wanda ya sanya ya zama shi ne babban jami’in diplomasiya da ya kai ziyara kasar a tsawon shekaru.

Kuma mataki yazo ne duk da hujjoji da ake da su na laifukan yaki, cin zarafin dan adam da kungiyar HTS ta yi musamman ma kan kabilu marasa rinjaye irin su alawiyyawa wanda suke fuskantar gallazawa daga bangaren gwamnati.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted