Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D

Babban jam’in hukumar tsaro ta kasar iran ya bayyana jin dadin kasar iran ga kasar Rasha saboda goyon bayan da ta bata a kwamitin sulhu

Babban jam’in hukumar tsaro ta kasar iran ya bayyana jin dadin kasar iran ga kasar Rasha saboda goyon bayan da ta bata a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya kan hakkin iran a gaban kasashen turai dake kokarin kakkaba mata sabon takunkumin karya tattalin Arziki,

Babban sakataren tsaro na kasar Iran Dr Ali Larijani ya fadi hakan ne a jiya talata A wata ganawa da yayi da jakadan shugaban kasar Rasha Alexander Lavrentiev da ya kawo ziyara nan kasar iran , larijani a matsayinsa na mai bawa jagora shawara ya jinjinawa kasar rasha game da goyon bayan da take bawa kwamitin.

LarIjani da sauran jami’an gwamnatin kasar Rasha sun yi bitar matakin hadin guiwa dake tsakanin Tehran da mosko a matakin kasa da kasa da kuma sauran bangarorin daban daban na ci ba a yankin,

Jakadan ya bayyanawa jami’an gwamnatin kasar iran  yanayin da ake ciki a yankin  a baya bayan nan, da kuma hanyoyin da za’a bi wajen kara karfi don  yin aiki tare. Kuma zaman ya zo ne yan kwanaki bayan da larijani ya gana da shugaban kasar Rasha viladmir putin a mosko inda ya mika masa sakon jagora kai tsaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted