Grossi: Za a iya warware batun Shirin nukiliyar Iran ne kawai ta hanyar diflomasiyya

Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a iya warware takkadama kan shirin Iran na

Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a iya warware takkadama kan shirin Iran na makamashin nukiliya ne ta hanyar diflomasiyya kadai.

Grossi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Neue Zeitung ta kasar Switzerland a jiya Lahadi.

Shugaban hukumar ta IAEA ya ce, masu binciken ba su sami wata shaida da ke nuna cewa Iran ta boye wani adadi na sinadarin uranium da aka inganta ba.

Ya kara da cewa, “Yawancin abubuwan da aka samu na Iran an adana su ne a wuraren da aka sani a Isfahan da Fordow, da kuma wani lokaci a Natanz.” in ji shi.

Grossi ya bayyana kwarin gwiwa cewa “za a gano wata hanyar diflomasiyya ta warware  takaddamar da ke tattare da shirin nukiliyar na Iran.”

“Dawo da dukkan bangarorin da ke takaddama a kan teburin tattaunawa zai iya ceton mu daga wani hadari na barkewar wani sabon yaki a nan gaba, in ji Grossi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted