Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya wallafa sako a shafinsa yana cewa ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Vladmir Putin akan yiyuwar za su gana da juna a birnin Budapest na kasar Haugary, domin lalubo hanyar kawo karshen yakin Ukiraniya.
Shugaban kasar na Amurka ya kuma bayyana tattaunawar da su ka yi a jiya Ahamis da Vladmir Putin da cewa ta yi amfani matuka, kuma na sami ci gaba.
Har ila yau shugaba Donald Trump ya ce; Su biyun sun amince da cewa a mako mai zuwa manyan jami’an kasarshen biyu za su gana da juna,kuma ministan harkokin wajensa Marco Rubio ne zai jagoranci tawagar Amurkan.
A gefe daya a yau Juma’a ne ake sa ran yin ganawa a tsakanin shugaban kasar ta Amurka da takwaransa na Ukiraniya Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy a fadar White House. Majiya Amurka ta ce a yayin ganawar, shugaba Trump zai tattauna yadda ganawa ta kasance a tsakaninsa da Vladmir Putin na Rasha.
Akan batun makamai masu linzami da Amurka ta bai wa Ukiraniya, shugaban kasar Rasha ya jaddada cewa, babu wani sauyi da hakan zai haifar a filin yaki, illa iyaka zai gurbata alakar Moscow da Washington.