Rahotanni daga Madagaska na cewa sojoji sun sanar da karbe mulki bayan arcewar shugaban kasar Andry Rajoelina.
Kanar Michael Randrianirina ya sanar a gaban fadar shugaban kasar cewa sojoji sun kwace mulki, da rusa majalisar dattawa da kuma babbar kotun tsarin mulkin kasar, yayin da ya bayyana yadda za a kula da majalisar dokokin kasar.
Hakan dai na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar tsige shugaba Andry Rajoelina da gagarumin rinjaye.
Sojojin na CAPSAT sun kuma sanar da cewa, suna kafa majalisar shugabannin kasa, wanda ya kunshi jamiāan soji da na Jandarmomi kadai.
A ranar 25 ga Satumba, ne aka fara zanga-zangar a Madagascar, kan katsewar ruwa da wutar lantarki wanda ya rikide zuwa bore wa gwamnati.
Shugaban kasar Andry Rajoelina, mai shekaru 51, ya yi kokarin shawo kan masu zanga zangar saidai hakarsa ba ta cimma ruwa ba, har zuwa lokacin da aka ga wasu sojoji sun shiga suna marawa masu zanga zangar baya.
Bayanai sun ce a ranar Lahadin da ta gabata ne wani jirgin sojin Faransa ya fitar da shugaban kasar Andry Rajoelina daga kasar.