Trump Ya ce An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Yakin Gaza

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da matakin farko na yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da matakin farko na yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

A wani sako da ya wallafa a kafarsa ta sada zumunta ya ce hakan na nufin nan ba da jimawa ba za a saki dukkanin wadanda ake garkuwa da su, sannan Isra’ila za ta janye dakarunta.

Ya ce wannan mataki ne na farko na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa. “Za a yi wa kowane bangare adalci,” in ji Trump. Kungiyar Hamas ta tabbatar da cimma yarjejeniyar ta kawo karshen yakin Gaza bayan tattaunawa kan yarjejeniyar Donald Trump.

Hamas ta ce yarjejeniyar ta kunshi janyewar Isra’ila daga yankin da kuma musayar fursunoni da kuma mutanen da aka yi garkuwa da su.

 Trump ya ce wannan babbar rana ce ga kasashen Larawaba da na Musulmi da Isra’ila da dukkanin kasashe da kuma Amurka. Sannan ya gode wa kasashen Qatar da Masar da Turkiya da ke shiga tsakani a tattaunawar tsakanin Hamas da wakilan Isra’ila da na Amurka.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da shugaba Trump ya ce yana tunanin kai ziyara yankin Gabas Ta Tsakiya a karshen mako domin ganawa da kasar Masar a inda ake tattaunawar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted