Hizbullah: Iran Ba Ta Taba Tsoma Baki A Cikin Kudurorinmu Ba

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da tashar Al Mayadeen, daya daga cikin m manyan kusoshin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyed Abdullah

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da tashar Al Mayadeen, daya daga cikin m manyan kusoshin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyed Abdullah Safieddine, ya yi magana kan lamurra da suka shafi harkokin gudanawa na cikin gida na kungiyar, da kuma shugabancinta a karkashin Sheikh Naim Qassem, da kuma dangantakarsu da  Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Safieddine ya  jaddada cewa Iran ba ta taba tsoma baki a cikin harkokin aiki ko na soja na kungiyar Hizbullah ba, yana mai cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci bai taba tsoma baki cikin duk wani matakin soji ba, yana daukar Sayyed Hassan Nasrallah a matsayin mai yanke shawara ta karshe a kan dukkanin batutuwa na kungiyar.

Ya kara da cewa a lokacin yakin Yulin 2006, a lokacin da makiya  suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Labanon, Jagoran ya kasance a birnin Mashhad, inda ya kira kwamitin tsaron kasa da manyan jami’an kasar ya shaida musu cewa an fara yakin, ya umarce su da cewa: ‘Ku je ku tambayi Sayyed Hassan da Hizbullah abin da suke bukata na dauki domin ci gaba da yin tsayin daka domin samun  nasara.

Ya ce babu wani umarni da Iran take baiwa Hizbullah, illa dai kawai ta kan bayar da nata taimakon da Hizbullah take bukata ne kawai ba ta tare da tsoma baki kan kudurorin kungiyar ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted