Iran na goyan bayan duk wani shiri da zai samar da ‘yancin Falasdinawa

Iran ta sanar cewa tana goyon bayan “duk wani shiri” da zai ba da damar samar da ‘yancin kai ga al’ummar Falasdinu, gabanin tattaunawa da

Iran ta sanar cewa tana goyon bayan “duk wani shiri” da zai ba da damar samar da ‘yancin kai ga al’ummar Falasdinu, gabanin tattaunawa da ake shirin farawa a Masar tsakanin Isra’ila da Hamas da nufin kawo karshen yakin zirin Gaza.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, iran ta ce “a ko da yaushe tana goyon bayan duk wani yunkuri na kawo karshen laifukan yaki, da cin zarafin bil’adama a Gaza da duk wani yunkuri na share fagen tabbatar da ‘yancin kai na al’ummar Palasdinu.”

Sanarwar ta ce, tilas ne yanke duk wata shawara kan tsagaita bude wuta ko sasantawa ta siyasa ta rataya a wuyan Falasdinawa da kansu.

Tehran ta ce tana maraba da duk wani matakin da aka dauka wanda ya kunshi dakatar da kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa, da janyewar sojojin yahudawan sahyoniyawan ‘yan mamaya daga Gaza, da mutunta hakkin al’ummar Falasdinu na cin gashin kansu, shigar da agajin jin kai da sake gina Gaza.

Sanarwar dai na tamkar maida martini ne kan shirin tsagaita bude wuta ga Gaza da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, wanda ya bukaci a gaggauta sakin wadanda da ake garkuwa da su a Gaza, da janyewar sojojin Isra’ila, da kuma kafa gwamnatin rikon kwarya.

A ranar Juma’a ne, Hamas ta gabatar da martaninta kan shawarwari 20 da Trump ya gabatar, inda kungiyar ta amince ta mika ragamar mulkin yankin da aka yi wa kawanya, tare da kubutar da sakin dukkan Isra’ilawa da ke tsare. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted