Janar Qa’ani: An Boye Ranar Fara Yakin Tufanul Aksa Har Haniyya Bai Da Labarisa

Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus’” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban

Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka, a jiya jumm’a a hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida a nan Iran. Ya kumakara da cewa a lokacinda aka fara yakin shugaban kungiyar ta Hamas yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Iraki, yana dawowa ne ya ji labarin fara shi.

Janar Qa’ani ya kara da cewa, amma  duk da haka, shahida Nasarallah ya zauna da abokan aikinsa a kungiyar suka fidda matsayi da kuma matakin da zasu dauka a cikin yini guda. Wanda kuma shine tallafawa kungiyar Hamas a yakin kwana guda bayan ta kaddamar da yakin.

Ya ce a cikin makonni 2 na farko na fara yakin Shahid sayyid Hassan Nasarallah ya ki yin magana wa jama’a, wannan ma wani takurawa ne ga ita HKI.  Ya cewa dakarun Hizbulla a cikin makonni na farko da fara yakin sun kashe kasha 1/3 na sojojin HKI da suke kudancin kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted