Mutane 4 ne suka rasa rayukansu a harin da wani ya kai kan wurin bautar yahudawa a birnin Manchester na kasar Burtaniya a cikin wadanda aka kashe har da mai gadin wurin bautar. Sannan yansanda sun kashe wanda ya kai harin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin labarai daga birnin Manchester, birni na 3 a girma a kasar Burtaniya na cewa , an kai harin ne a wurin bauta na yahudawa na Crumpsall a tsakiyar birnin. Hakama firai ministan kasar ta Burtaniya Keir Starmer ya yanke ziyarar aiki da yake yi a birnin Copenhegen ya dawo London don jajorantar majalisar ‘Cobra Meeting’ don tattauna baton harin.
Shugaban yansanda masu yaki da ayyukan ta’addanci Lawrence Taylor ya bayyana cewa hare-harin Crumpsall aikin ta’addanci ne sannan ya zo a dai-dai rana mafi muhimmanci ga yahudawa.