Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran Yace SnapBack Baya Bisa Ka’ida

Mohammad Bakir Qalibof kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa abinda kasashen turai uku suka yi na amfani da Snapback baya bisa ka’ida kuma

Mohammad Bakir Qalibof kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa abinda kasashen turai uku suka yi na amfani da Snapback baya bisa ka’ida kuma Iran ba zata kiyayesu ba.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa kasashen Rasha da China wadanda suka kasance mambobi na din din din a kwamitin tsaro na MDD sun tabbatar da cewa abinda turawan suka yi baya bisa ka’ida.

Ya ce idan wadannan kasashe da Amurka suka dauke wani bataki kan Iran, iran zata maida martini mai tsanani a kansu.

Qalibof ya bayyana cewa kasashen sun yi amfani da tattaunawa da a matsayin makami don cimma manufarsu da durkusarwa da kuma takurawa  gwamnatin JMI. Ya kara da cewa sun yi watsi da dukkan kokarin da JMI ta yi na kaucewa sabani tsakaninsu, daga ciki har da yarjeniyar alkahira da hukumar IAEA.

 Daga karshe ya bayyana cewa, idan HKI bata sake kawowa JMI hare-hare ba, don snapback bas ai dai ta san cewa idan ta sake kawowa kasar Iran hare, a wannan karon sai ta gamu da maida martini mafi tsanani da ta farko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted