Sojojin Yemen sun kaddamar da mummunan farmaki kan yankin Jaffa da makami mai linzami
Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Alhamis cewa; Sun kai hari da makami mai linzami kan yankin Jaffa da aka mamaye.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Yemen ta fitar ta tabbatar da cewa: Rundunar sojinta ta kai wani harin soji mai inganci ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2 mai dauke da kawuna da dama, inda harin ya yi mummunan barna a yankin Jaffa da aka mamaye. Sanarwar ta kara da cewa, wannan farmakin ya samu nasarar cimma manufofinsa, kuma ya sa miliyoyin garken yahudawan sahayoniyya sun tsere zuwa matsugunin karkashin kasa tare da dakatar da zirga-zirga a filin jirgin sama na Lod.
Rundunar ta kara da cewa, godiyan Allah, sojojin tsaron sama sun samu nasarar dakile wasu hare-hare ta hanyar harba makamai masu linzami daga sama zuwa sama, a lokacin farmakin da rundunar sojin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Yemen a baya-bayan nan, lamarin da ya tilastawa wasu jama’a barin wajen tare da dakile wani bangare na harin.