Sauye-Sauyen Siriya A hannun Amurka Da Aika’ida

Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar yan ta’adda ta Deash kuma kungiya mafi kiyayya ga Amurka a fadin ta a yau ya kama hanya zuwa NewYork

Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar yan ta’adda ta Deash kuma kungiya mafi kiyayya ga Amurka a fadin ta a yau ya kama hanya zuwa NewYork don gabatar da jawabin a babban zauren MDD a karon farko.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, tun lokacinda tawagar Amurka ta ziyarci kasar Siriya bayan kifar da gwamnatin shugaba Bashar Al-Asad a shekarar da da ta gabata, shugaban tawagar  Barbara Leaf mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka na lokacin, bayan ganawa da Abu Muhammad Julani, ta bada sanarwan gwamnatin Amurka ta dauke ladar kudede miliyon $10,000 wanda ta saka don a kawo mata kan Abu Muhammad Al-julani shugaban kungiyar Al-ka’isa bayan hare-haren 11 ga watan satumban shekara ta 2001. Ya kuma canza sunansa zuwa Ahmad Ashar’a.

Labarin ya kara da cewa a halin yanzu Amurka ta bashi Visa inda za iyi jawabi a babban zauren MDD. An kashe mutane akalla 3000 a hare-haren na 11 ga watan Satumba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted