Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza.

Mohammad Hindi mataimakin sakatare janar din kungiyar gwagwarmaya ta jihadil Islami ya bayyana cewa an karbi bukatar dakatar da bude wuta a gaza, amma kasar

Mohammad Hindi mataimakin sakatare janar din kungiyar gwagwarmaya ta jihadil Islami ya bayyana cewa an karbi bukatar dakatar da bude wuta a gaza, amma kasar Amurka da kasashen turai basa son a dakatar da bude wuta har sai an kawar da dukkan kungiyoyin gwagwarmaya baki daya ba wai a yankin falasdinu ba kawai.

Haka zali ya kara da cewa HKI ta kai hari kan wajen da wakilan kungiyar hamas  suke a  birnin doha na kasar Qatar don tattaunawa kan batun dakatar da bude wuta.

Isra’ila ta sanar a hukumance cewa prime minister Natanyaho  ya sanar da shugaban Amurka Donald trump  jim kadan kafin kai harin cewa isra’ila za ta kai wa Qatar hari,

Harin ya jawo nuna damuwa sosai kan batun tsaro a kasashen larabawa na yakin tekun fasha bayan da Isra’ila ta lallata yankin Gaza kuma ta wuce gona da iri kan kasashen Iran Labanon Qatar, siriya da kuma Yamen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted