Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.

Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a mastayin babban birni.

Har ila yau kungiyar ta yi kira da a kara daukar matakan ladabtarwa kan Isra’ila tare da hukunta shugabanninta kan laifukan cin zarafin bil’adama.

Sanarwar ta soki gwamnatin Isra’ila kan yadda take ci gaba da yin watsi da dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin jin kai, tare da bayyana “mummunan cin zarafi” da ake yi wa Falasdinawa.

An fitar da wannan sanarwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun sakar diflomasiyya tsakanin kasashen dake amincewa da Falasdinu a matsayin kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted