Iran Da Pakistan Sun Sake Tsara Dangantakarsu Ta Tattalin Arziki

Kasashen Pakistan da Iran suna shirin fadada dangantakar tattalin arzikin da ke tsakanin daga dalar Amurka biliyon $3 a ko wace shekara zuwa dalar Amurka

Kasashen Pakistan da Iran suna shirin fadada dangantakar tattalin arzikin da ke tsakanin daga dalar Amurka biliyon $3 a ko wace shekara zuwa dalar Amurka billion $10.

plan to expand bilateral trade from its current level of just over $3 billion to an ambitious $10 billion. Tashar talabijan ta Presstv a nan ta nakalto bangarorin biyu na fadar haka ne a yau Lahadi, a taron kwamitin tattalin arziki na hadin giwa tsakanin kasashen biyu karo na 22nd da aka gudanar a nan Tehran.

Labarin ya kara da cewa, kasashen biyu sun amince da cewa, halin da harkokin tattalin arziki tsakanin sub a na gaskiya bane,   tunda a kwai bangarori da dama dabasu taba ba, ko kuma yi magana a kansu ba. 

Kwamitin ya bayyana cewa, akwai al-amura na kasuwanci masu muhimanci a bangarorin biyu wadanda ba’a tabosu ba, kuma sun hada da cibiyoyin kasuwanci, kungiyoyin yan kasuwa na kasashen biyu, samar da kasuwannin hadin giwa na kan bodojin kasashen biyu, fadada kasuwancin kan iyakokin kasashen biyu, samar da hulda tsakanin kamfanonin kasashen biyu. Kafa kamfanoni na hadin giwa da sauransu. Sannan a watan da ya gabata ne kasashen Iran, Turkiyya da Pakistan suke maganar Farfado da layin dogo daga Istambul Teran zua Islamabad a ko wani wata, wanda kuma yake cikin shirin kungiyar tattalin arziki na yankin ta (ECO). Jirgin da farko na jigilar kaya ne kawai kafin  a yi maganar mutane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted