Isara’ila Ta Kaddamar Da Shirin Iko Da Wasu Yankuna A Yammacin Kogin Jodan.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin sahyuniya ta gaddamar da shirin mamaye wasu sabbin yankuna a kusa da birnin Qudus inda ta mamaye yankuna guda 3

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin sahyuniya ta gaddamar da shirin mamaye wasu sabbin yankuna a kusa da birnin Qudus inda ta mamaye yankuna guda 3 kuma ta bukaci falasdinawa neman izini kafin su shiga gidajensu.

Wannan mataki ya canza ka’idar mallakar kasa, bayan da Isra’ila ke kokarin kwace iko da muhimman wurare a gabar yammacin kogin jodan, wanda zai yi illa sosai ga yiyuwar samun kasar falasdinu mai cin gashin kai .

Ana su bangaren hukumomin falasdinawa sun yi tir da wannan mataki, kuma sun bayyana shi a matsayin mataki mai muhimmacin wajen hade birnin Qudus da sauran yankunan falasdinawa ,kuma take hakokin falasdinawa ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted