Kididdigar da aka fitar akan adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da kuma jikkata sun haura 230,000,wanda ya faro tun daga watan oktoba 2023.
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ce ta fitar da wannan kididdigar a jiya Juma’a, sannan kuma ta bayyana cewa an kara samin wani adadi mai yawa na shahidai a cikin sa’oi 24, yayin da wasu 146 su ka jikkata.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza din ta kuma bayyana cewa; Da akwai ma’aikatan agaji da suke aiki tukuru domin fito da shahidan da suke kwance a karkashin baraguzai.
A fagen yunwa da take ci gaba da daukar rayukan mutanen Gaza kuwa, ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza, ta ce, an sami Karin wasu shahidai 4 da yunwa ta kashe da hakan ya kai adadinsu zuwa 440,daga cikinsu da kananan yara 147.
A nata gefen, hukumar kiwon lafiya ta duniya ( w.h.o) ta yi gargadi akan durkushewar cibiyoyin kiwon lafiya a yankin saboda rashin kayan aiki da makamashi.