Sheikh Na’im Kassim Ya Kira Yi Saudiyya Da Ta  Bude Sabon Shafi Da Gwagwarmaya

Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi

Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya  juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da bunkasa ta fuskokin ttatalin arzki, siyasa da al’adu da ci gaba.

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya kira yi kasar Saudiyya da ta bude sabon shafin alakarta da kungiyoyin gwagwarmaya.

Har ila yau Sheikh Na’im Kassim ya ce, HKI wani makami ne na kasashen turai da aikinsa shi ne yin kisan kare dangi akan duk wanda ya ki yin biyayya a gare su.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya yi ishara da yadda Amurka da ‘yan mulkin mallakar turai suke ci gaba da bayar da cikakken taimako a kisan kiyashin da take yi, da kuma karya dokokin kasa da kasa.

Haka nan kuma babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya bayyana yadda Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya furta cewa yana son ganin kafuwar “ Babbar Isra’ila” da sauya iyakokin wannan yankin da rusa Hamas sannan kuma da korar Falasdinawa daga Gaza. Haka nan kuma matakin gaba na HKI shi ne sake mamaye yankin yammacin kogin Jordan.

A kan harin da HKI ta kai wa Qatar, Sheikh Na’im Kassim ya ce hakan yana kara nuni ne da manufar samar da faffadar Isra’ila.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted