Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kaddamar da hare-hare guda 3 da gagarumar nasara a wasu mihimman wurare a HKI, da zimmar mayar da martani kan hare haren da Isra’ilan take kai mata, saboda ci gaba da nuna goyon bayan alummar falasdinu da take yi da ta kwashe shekaru biyu ta na yi musu kissan gilla,
Acikin wani bayani da kakakin sojin kasar Yamen Yahya Saree ya fitar ya sanar cewa kasarsa ta kaddamar da hare hare a muhimman wuraren guda 3 a Yaffa da HKI ta mamaye , kuma ta yi amfani da makami na haypersoni balisstic missile da ta basu suna da falasdinu na 2.
Haka zakila ta kai hari a yankin umm Rashrash wato Eilat inda ta yi amfani da jirage marasa matuki guda 3, da kuma Be’er sheva, sai dai yace za su ci gaba dakai har a Eilit ba kakkautawa. Kasar yamman ta sha alwashin ci gaba da kai hare-haren nuna goyon baya ga alummar falasdinu da ake zalunta har sai HKi ta dakatar da kisan kare dangi da take yi a gaza kuma a dauke killacewar da aka yi mata.