Sharhin Bayan Labarai: Qatar Zata Sauya Amurka A Matsayin Abokiyar Tsaron

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’. A ranar Alhamis da ta gabata ce, shafin yanar gizo na Acios na labarai ya nakalto Firay ministan kasar Qatar tana fadawa  fadar white House kan cewa, bayan saba alkawalin da Washington ta yi, dangane da hare-haren da HKI ta kaiwa birnin Doha, Qatar zata sake duba yarjeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amurka ta kuma nemi sabon abokin aiki a wannan bangaren.

Axious ta kara da cewa, tunda Benyamin Natanyaho bai tuntubi Washington ko Trump ko kuma wani babban Jami’an gwamnatinsa kafin ya kai hare-haren da ya kai kan doha,!, al-amarin ya fi hatsari idan ya zo kan kasashen duniya, wadanda suka dogara da Amurka don tsaron kasashensu. Anan Amurka zata rasa aminci da yardar da take da shi take da shi  daga  wasu kasashenata.

Labarin ya kara da cewa Firay ministan kasar ta Qatar Muhammad bin Abdurrahman bin Jassim Al-thani, ya fadawa fadar whitehouse, bayan wannan yaudarar kasarsa zata nemi wani amintacce wanda zai maye gurbin Amurka.

Al-thani ya fadawa tashar talabijan ta CNN kan cewa a halin yanzu kasashen larabawa na yankin tekun farisa suna tattauna yadda zasu maida martani ga wannan al-amarin saboda wasu kasashen yankin da dama suna dogaro da Amurka don tabbatar da tsaron kasashensu. Don haka hare-hare kan Doha ya shafi dukkan wadan nan kasashe.

Har’ila yau rahoton ya bayyana cewa, bayan hare-haren da JMI ta kaiwa Al-udait ‘Air Base” a cikin yakin kwanaki 12 wanda Amurka ta jefa boma-bomai kan cibiyar makamashin nukliya na kasar, da kuma hare-haren da HKI kan Doha, Qatar tana ganin dole ta sake lalen harkokin tsaron kasar.

Rahoton ya ce, Al Thani ya fadawa Steve Witkoff, jakadan Amurka na musamman a gabas ta tsakiya kan cewa, Qatar zata sake duba harkokin tsaron kasar , musamman tare da Amurka saboda samun cikekken tsaro ga kasar.

Dangane da wannan shafin yanar gizo na labarai ‘Axios ta sami wani bayani da ke cewa shugaban Trump ya bukuci Natanyahu ya dauki alkali ba zai sake kaiwa kasar Qatar hare-hare ba.

Sannan bayan haka, Natanyahu bai nemi Afwar kasar Qatar ba, kuma ya ma yi alkawalin zai sake kai wasu hare-haren a kan doha idan bukatar haka ta kama.

 Qatar dai itace kasar Larabawa ta 7  wacce HKI ta yiwa ruwan boma bomai tun bayana fara yaki a gaza a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta, banda Gaza da yankin yamma da kogin Jordan, yahudawan sun kai hare-hare kan Lebanon, Syriya Iraki, Iran da kuma ita Qatar

Axios ya bayyana cewa a ranar Talatan da Natanyahu ya kai hare-hare kan Doha, shugaba Trump ya kira Natanyahu ta wayar tarho, har sau biyu, da farko yay a bayyana rashin aqmincewa da kai hare-haren, sannan tare da tambayarsa menene amfani na dogon zangon da HKI zata samu,

Wani tsohon jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa, Firay ministan kasar Qatar ya na daukar hare-haren a matsayin yaudara daga Tel’viv da kuma washingtong gaba daya.

Banda haka Benyamin Natanyahu ya fito a ranar Laraba yana fadar cewa yayi dai dai a hare-haren da ya kai Doha, sannan idan yan kungiyar Hamas sun ci gaba da kasancewa a kasar Qatar zai sake kai masu hare-hare.

Sannan ya kara da cewa hare-harensa a kan doha yana dai dai da hare-haren Amurka a kan Afganistan da Pakistan a lokacinda take neman  kungiyar Al-Qaeda bayan   ga watan Satumba.

Al-thani ya fadawa CNN kan cewa dole a hukunta Natanyahu, saboda keta hurumin kasa mai cikekken yanzi, wanda yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa tare da kiranta Yar ta’adda.

Daga karshe Althani ya bayyana cewa, a halin yanzu tana tattaunawa da sauran kasashen larabawa na yankin tekun farisa, inda zasu iya maida martanin da zai sanya yankin shiga hatsari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted