Mutane 5 Sun mutu, 20 Sun Jikkata Sakamakon Harin Neman Shahada A Isra’ila.

Bayan barazanar da ministan yaki na HKI yayi na yin ruwan bama-bamai kan yankin Gaza wato kai hari kan manyan manyan gine –gine dake yankin

Bayan barazanar da ministan yaki na HKI yayi na yin ruwan bama-bamai kan yankin Gaza wato kai hari kan manyan manyan gine –gine dake yankin , sai gashi kafafen yada labarai na isra’ila sun sanar da wani harin neman shahada da aka kai a birnin Qudus inda yahudawa 5 suka mutu guda 20 kuma suka jikkata

Gidajen talabijin na HKI sun sanar da adadin wadanda abin ya shafa sakamakon harin  sun bayyana cewa mutane 5 ne suka mutu sai kuma 20 suka yi jikkata, yayin da halin 6 daga cikinsu rai kwakwai mutu kwakwai.

Sai dai wannan yana zuwa ne bayan da ministan yaki na HKI Yasrail Katsi yayi barazana ga kungiyar Hamas cewa idan basu mika makamansu ba, kuma basu saki fursunonin yaki ba, to za su rusa gaza baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted