An Rufe Kamfanin Kera Makamai Na Isra’ila Dake Birtaniya.

Rahotani sun bayyana cewa an rufe kamfanin kera makamai na HKI dake birtaniya mai suna  Elbit system sakamakon zanga-zangar da kungiyoyin sakai da masu goyon

Rahotani sun bayyana cewa an rufe kamfanin kera makamai na HKI dake birtaniya mai suna  Elbit system sakamakon zanga-zangar da kungiyoyin sakai da masu goyon bayan palasdinu suka yi karkashin dokar yaki da ta’addanci a birtaniya.

Wannan mataki yayi tasiri sosai a duniya inda dubban mutane ke ci gaba da matsin lamba ga gwamnatocinsu da su yanke duk wata alakar kasuwanci da isra’ila sakamakon ci gaba da kisan kare dangi kan alummar Gaza.

Shi dai kamfanin Elbit System dake birtaniya na yanar gizo na Bristol ya fara aiki ne a karkashin wata yarjejeniyar tun a shekara ta 2019 zuwa ta2029  Kamfanin shi ne babban mai samar da jirage marasa matuka da sojojin Isra’ila ke amfani da su, musamman a yankin  Gaza. Abubuwan da yake yi sun hada da fasahar jiragen sama, jiragen ruwa, da fasahar yaki na kasa, da kuma tsarin bada umarni da kuma sarrafawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted