Trump Zai Sauya wa Ma’aikatar Tsaro Suna Zuwa Ma’aikatar Yaƙi

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce a yau Juma’a, shugaba Amurka Donal Trump zai rattaba hannu kan wata doka da za ta sauya

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce a yau Juma’a, shugaba Amurka Donal Trump zai rattaba hannu kan wata doka da za ta sauya sunan ma’aikatar tsaron kasar zuwa ma’aikatar yaki.

Canjin suna na dindindin na buƙatar Izinin majalisa, to amma umarnin zartarwa da shugaban zai sa wa hannu, zai ba da damar amfani da sunan na wucin gadi.

A wata hira da aka yi da shi, sakataren tsaron kasar Pete Hegseth, ya ce hakan zai nuna wani sauyi da ke nufin ma’aikatar tsaron kasar ta Pentagon ta rungumi wani suna na Jarumta.

Ya ce ko nasarorin da kasar ta samu a yakin duniya na daya da na biyu ta same su ne da sunan Ma’aikatar Yaki, ba wai Ma’aikatar tsaro ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted