Jami’in Siyasar Kungiyar Hamas Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Shugaban Amurka

Jami’in siyasar kungiyar Hamas ya mayar da martani ga shugaban kasar Amurka Trump cewa: Netanyahu yana son yaki mara iyaka ne Mamba a ofishin siyasa

Jami’in siyasar kungiyar Hamas ya mayar da martani ga shugaban kasar Amurka Trump cewa: Netanyahu yana son yaki mara iyaka ne

Mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas Izzat al-Rishq ya fada a yammacin jiya Laraba, yayin da yake mayar da martani ga bukatar shugaban Amurka Donald Trump na sakin dukkan fursunonin Isra’ila, cewa “Hamas ta amince a ranar 18 ga watan Agusta kan shawarar masu shiga tsakani, wadda ta dogara ne kan shawarar Witkoff, kuma har yanzu Netanyahu bai bayyana matsayinsa ba.”

A martanin da ya gabatar kan furucin Trump, al-Rishq ya tabbatar da cewa, kungiyar Hamas ta bayyana shirinta na cimma cikakkiyar yarjejeniya, inda za a saki dukkan fursunonin, a madadin adadin da aka amince na fursunonin Falasdinu da ke gidajen yarin Isra’ila, ta hanyar da za ta cimma tsagaita bude wuta da kuma janyewar sojojin mamayar Isra’ila daga Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted