Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Babu aminci tsakanin kasar Iran da Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: An rasa amana tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, yana mai jaddada cewa; “Iran ba ta maraba da mayar da takunkumin kan kasarta, amma ta koyi yadda za ta kare mutuncin al’ummarta da fuskantar wannan yaki na rashin adalci.”
Dangane da yiwuwar sake wani yaki kuwa, ya ce, “Iran a shirye take.” Hakan ya zo ne a wata hira da jaridar Guardian ta yi da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i.
Game da sharuɗɗa uku da Turai ta sanar don yin shawarwari, Baqa’i ya ce: “A ganinsa, waɗannan yanayi suna nuna rashin muhimmancinsu da kuma rashin kyakkyawar niyyarsu. Ku tuna, Iran tana tsakiyar cikin tsarin diflomasiyya a lokacin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kaddamar da hari kan kasarta, tare da haɗin gwiwar Amurka kuma mai yiwuwa tare da sanin kasashen Turai uku. Don haka, ko ta yaya, duk sun amince da harin.”