Rundunar sojin Yaman ta sanar da cewa ta kaddamar da wasu manyan hare-hare a kan wasu mihimamn wurare na tsaro da tattalin arzikin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Tun a ranar Litinin da ta gabata ta sanar da cewa za ta aiwatar da ayyukan soji biyar masu girma a kan wasu muhimman wurare da suka hada da hedikwatar tsaro, tashar wutar lantarki ta Hadera, filin sauka da tashin jiragen sama na Lod da ke Jaffa ko Tel Aviv, da kuma tashar jiragen ruwa ta Ashdod, da kuma tashr jiragen ruwa ta MSC ABY da ke arewacin tekun Bahar Maliya. An gudanar da ayyukan ta hanyar amfani da jirage marasa matuka da dama da kuma makamai masu linzami.
Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree a cikin wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da cewa, sojojin sun gudanar da ayyuka hudu ta hanyar amfani da jiragen Sammad 4 marasa matuka.
Dakarun Yaman sun tabbatar da cewa wadannan hare-hare na daga cikin ayyukan da suke yin a ci gaba da goyon baya da taimakon al’ummar Palasdinu a zirin Gaza har sai an daina kai musu hare-hare tare da kawo karshen killacewar da ake yi wa yankin.
Sannan kuma ya yi ishara da cewa a lokaci guda hare-hare wani bangare ne na ayyukan ramuwar gayya da aka fara aiwatarwa kan kisan firayi minister da kuma wasu ministoci gami da jami’an gwamnatin Yemen da Isra’ila ta aikata.