Fiye Da Mutane 1000 Ne Suka Rasa Rayukansu A Yammacin Sudan Saboda Zaizeyar Kasa

Mutanen sudann daga yammacin kasar kimani dubu guda ne suka raya rayukansu sanadiyyar zai-zayar kasa, kuma kan tsaunukan Marre. Shafin yanar gizo na labarai Arab

Mutanen sudann daga yammacin kasar kimani dubu guda ne suka raya rayukansu sanadiyyar zai-zayar kasa, kuma kan tsaunukan Marre.

Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Abdulwahid Muhammad Nour na kungiyar ‘The  Sudan Libration Movementa’ Wato (SLM) wacce take iko da yankin yana fadar haka. Ya kuma kare da cewa, zaizeyar kasa ta aukune bayan ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a yankin. Ya kuma kammala da cewa mutum guda ne kacal ya tsira da ransa a garin Marra dake kan tsaunin.

Kungiyar ta bukaci taimakon MDD da kuma sauran kungiyoyin Agaji a duniya don fidda gawakin mutanen da zaizayar kassar ta bisne a kan tsaurin.

Kasar Sudan dai tana cikin yaki fiye da shekaru biyu, inda garin Fasha na yankin Darfur yana karkashin ikon yan tawaye, ta yadda mutanen basu da mafaka in ban kan tsaunukan da suke yankin wadanda basu bukatun rayuwa a cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted