Kasar Venezuela ta sami sakon tallafi daga kasar Iran a lokacinda ministan harkokin wajen kasar Vanezuela ya gaba da jakadan Iran a Caracas.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun bayyana cewa zasu kara karfafa dangantaka ta musamman dake tsakaninsu na tsaro da sauran bangariri masu musammancin da ke tsakaninsu. Saboda kare diyaucinsu da kuma iko a kan kasashensu.
Ministan harkokin wajen Venezuela Efan Jeel ya bayyana cewa sun tattauna da Jakadan Iran a Venezuela Ali Shagni a ranar litinin da ta gabata.
Ministan ya kara da cewa Venezuela ta sami sakon tallafawa daga kasar Iran don tunkarar barazanar da kasar take fuskanta daga kasar Amurka.