Jack Neriya, tsohon shugaban hukumar leken asirin Isra’ila a Syria da Lebanon, ya yi gargadi game da masu tunann cewa ta yi rauni, yana mai jaddada cewa “kungiyar ta sake gina karfin soji kuma ba ta da niyyar yin watsi da makamanta.”
A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin, Neriya ya ce, “Tun daga watan Nuwamba, Hezbollah ta sake tsara sahunta, ta dawo kera jiragen sama marasa matuka da sauran makamanta, tare da jaddada kudurin ta na ci gaba da yin amfani da makamanta.”
Ya kara da cewa, bayyanar babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem a bainar jama’a a cikin kayan soji na nuni da daukar matakin da ya dace, musamman ma a lokacin da ake samun takun saka da musayar yawo tsakanin Amurka da Lebanon a cikin kwanakin nan.
Wannan takun saka dai ya bayyana ne a baya-bayan nan yayin da wakilin Amurka Tom Barrack ya soke ziyarar da ya kai Taya da al-Khiam sakamakon zanga-zangar da al’ummar yankunan biyu suka yi tare da nuna Rashin amincewasu da hankoron mulkin mallakar Amurka a kan kasarsu.
Ya kara da cewa, “Isra’ila” na neman daidaita alaka da Siriya, ganin cewa a halin yanzu Isra’ila tare da sabuwar gwamnatin Syria suna da abokan gaba da suka yi tarayya a kansu, wato Iran da Hizbullah,” wanda kuma hakan ya zo hatta a ta bakin shugaban rikon kwarya na Syria Ahmad al-Sharaa (Al-joulani), wanda ya taba cewa “Syria da Isra’ila suna da makiya daya, kuma za su iya taka muhimmiyar rawa tare wajen yaki da su.