A dazu-dazun nan ne aka kammala wani zagaye na tattaunawa tsakanin Iran da kuma kasashen turai uku, wato Faransa, Burtaniya da Jamus kan shirin Nukliyar kasar Iran da kuma daukewa JMI takunkuman tattalin arziki da kasashen suka dora mata.
Kamfanin dillancin labarai Iran Press ( IP) na kasar Iran ya bayyana cewa Majid Takht-Ravanchi da Kazem Gharib-Abadi ne suka wakilci kasar Iran a wannan tattaunawar, wanda har yanzun ba’a bayyana natijarsa ba. A yayinda mataimakan ministocin harkokin waje na kasashen turan uku suka wakilci kasashensu.
Tattaunawar ya maida hankali ne kan shirin Nukliyar kasar Iran a karkashin yarjeniyar JCPOA wanda kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231 yake goyon bayansa.
Kasashen turan dai sun tabbatar da cewa ba zasu taba hana Iran tashe makamashin Uranium tare da amfani da karfi ba, don sun ga yakke HKI da Amurka suka kasa yin haka.
Don haka a halin yanzu suna kokarin farfado da yarjeniyar JCPOA ne tare da kuduri mai lamba 2231 don daukewa Iran takunkuman da suka dora mata sannan su tabbatar da cewa Iran tana aiwatar da kudurin kamar yadda ya dace.