Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kasar Armeniya ta tabbatar da cewa babu wata barazana ga Iran daga yankinta
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Bangaren Armeniya ya tabbatar da cewa babu wata barazana ga Iran daga yankinsa.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da shawarwarin da aka yi tsakanin kasashen Iran da Armenia a matakin shugabannin kasashen biyu, Araqchi ya bayyana cewa: An yi shawarwari mai tsanani tsakanin bangarorin biyu, kuma sun yi tattaunawa mai ma’ana sosai, dangane da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin tattalin arziki, wanda yake da yawa, kamar kasuwanci, zuba hannun jari, da aiwatar da ayyukan fasaha da injiniya, da hadin gwiwar al’adu, wanda hakan ya kasance mai matukar muhimmanci ga al’adu tsakanin kasashen biyu.
Dangane da batutuwan da suka shafi zirga-zirgar jiragen sama da kuma tattaunawar da aka yi a baya-bayan nan a birnin Washington, Araqchi ya ce: Bangaren Armenia ya ba da cikakkun bayanai dalla-dalla tare da jaddada cikakken saninsa kan jajayen layukan kasar Iran, wadanda za su yi riko da su a kodayaushe, kuma Armeniya ba za ta taba bari a samu wata barazana ga Iran ta bullo daga kasarta ba, an amince da kammala cikakken daftarin aiki tare da manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu nan ba da jimawa ba.
A yayin ziyarar da shugaban kasar Iran ya kai a kasar Armeniya, manyan jami’an kasashen biyu sun rattaba hannu kan wata sanarwa ta hadin gwiwa da takardun hadin gwiwa guda goma a fannonin tattalin arziki, al’adu da siyasa daban-daban da nufin karfafa alaka.