Aragchi: Yiyuwan Sake Shiga Yaki Da HKI Nan Kusa Yana Da Wuya

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su shiga yaki a ko dauce, amma yana ganin yiyuwar a sake

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su shiga yaki a ko dauce, amma yana ganin yiyuwar a sake shiga yaki da HKI nan kusa yana da wuya.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Abbas Argchi yana fadar haka, a daren Ashamis da ta gabata, a lokacinda ya kai ziyarar Karbala don ziyarar 40 na Imam Hussain,(a)

Ministan ya bayyana cewa, a halin yanzu, mutanen kasar Iran suna da hadin kai a tsakaninsu da kuma gwamnatin kasar , yace makiya zasu so raba kan mutanen kasar da shuwagabanninsu da kuma sojojin kasar wadanda suke bada rayukansu don kare kasar da kuma kare mutanen kasar.

Ministan ya kammala da cewa a yakin da makiya zasu kawo mana, sun fuskanci maida martani mai tsananiĀ  baya. Ya ce a cikin yakin kwanaki 12 sojojin kasar cilla makamai masu linzami har zagaye 22.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted