Sudan: Al-Burhan ya ce babu sulhu tsakaninsu da dakarun RSF

Shugaban majaliasar gudanarwa na kasar Sudan kuma babban hafsan hafsan sojojin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya yi alkawarin fatattakar dkarun RSF, tare da kawar

Shugaban majaliasar gudanarwa na kasar Sudan kuma babban hafsan hafsan sojojin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya yi alkawarin fatattakar dkarun RSF, tare da kawar da “duk wata dama ta yin sulhu.”

Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyyay a bayar da rahoton cewa, al-Burhan ya ce sojojin za su ci gaba da yaki ko ta halin kaka, kuma ba za su ci amanar sadaukarwar wadanda aka kashe a rikicin ba.

Al-Burhan ya yaba da irin tsayin dakan da sojojin suka yi a manyan garuruwa irinsu El Fasher, Babanusa, da Kadugli, yana mai cewa suna ci gaba da kare kasar ta kowace fuska.

Majiyar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, Al-Burhan ya gabatar da wani fayil na tsaro da ke nuna yadda wasu kasashe  ke da hannu wajen tallafa wa Dakarun RSF da kudade, da horo.

Wannan dai na zuwa ne a yayin tattaunawar tsaro da aka gudanar a birnin Zurich na kasar Switzerland, tare da babban mai baiwa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin Larabawa, Gabas ta Tsakiya da Afirka, Massad Boulos.

Al-Burhan ya kuma tabbatar da cewa “yakin da ake yi a Sudan yana wakiltar wani shiri ne dake  nufin raba kan kasar Sudan,” yana mai jaddada cewa “Daular Sudan, da dakarunta da kuma kungiyoyin sa kai na jama’a sun tsaya tsayin daka don dakile wannan shiri.” Ya yi kira da a wargaza ‘yan bindiga, a rusa mambobinsu, a gurfanar da shugabanninsu gaban kuliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted