Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy

Miistan harkokin wajen kasar Masar ya sake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi  da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael

Miistan harkokin wajen kasar Masar ya sake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi  da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael Grossi ta wayar tarho.

Kamfanin dillancin labarana Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar na cewa jami’am gwamnatin kasashen biyu da kuma Grossi sun tattauna al-amura da suka shafi sake komawa kan taburin tattaunawa da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukliya ne bayan yakin kwanaki 12 wadanda HKI da Amurka suka kaiwa kasar Iran.

Badar Abdullatf ministan harkokin wajen kasar Masar yana kokarin sake maida dangantakar hukumar AIEA da kuma Iran bayan tayi tsami a watan yunin da ya gabata, inda Iran tana zargin Grossi da hada kai da Amurka da HKI a hare-haren da suka kaiwa JMI a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025.

A cikin makonnin da suka gabata jami’an gwamnatocin biyu sun tattauna da Grossi a kan wannan al-amari kafin ziyarar da mataimakin Grossi ya kawo nan Tehran a ranar litinin da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted