Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida 

Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida Sojojin Yemen

Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida

Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Talata cewa: Sun kai farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda shida, inda suka kai hari kan wasu muhimman wurare 4 na haramtacciyar kasar Isra’ila a yankunan Haifa, Negev, Umm al-Rashrash, da kuma Bi’ersheba na Falasdinu da aka mamaye.

Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa: “Ayyukan sun cimma nasarar cimma manufofinsu,” yana mai jaddada ci gaba da ayyukan bayar da tallafi har sai an daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza.

Sari’e ya ce: Ci gaba da aiwatar da shirin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi na da nufin kawar da al’ummar Falastinu ta hanyar kisan kiyashi da kakaba yunwa da tilasta musu gudun hijira daga mahaifansu zai haifar da mummunan sakamako ga dukkanin kasashen Larabawa da na musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted