Sojojin HKI sun shiga yankuna da dama a lardin Qunaitara na kasar Siriya a Jiya Asabar. Inda ta kafa shingaye a kan tituna a wasu garuruwa a lardin suka yi ta binciken ababen hawa, kafin su janye daga baya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, HKI tana shirin mamayar wadan nan yankunan na kasar Siriya shi ya sa bata son ganin an sami zaman lafiya a kasar ta Syriya gaba daya, har zuwa lokacinda zata mamaye yankin. Gwamnatin kasar Siriya mai ci ta tabbatar da cewa samuwar sojojin HKI a duk lokacinda suka ga dama a wadannan yankuna alamace ta rashin zaman lafiya a kasar.
Kowa ya san cewa HKI ba zata taba barin kasar Siriya ta zauna lafiya ba. Don zamn lafiya da hadin kan mutanen kasar hatsari ne a wajenta.