Tehran Times: Mai Yiwuwa Iran da Amurka su koma Tattaunawa

Jaridar Tehran Times, ta nakalto cewa, Iran da Amurka a shirye suke su fara wata sabuwar tattaunawa. Majiyoyin sun ce tattaunawar za ta kasance ba

Jaridar Tehran Times, ta nakalto cewa, Iran da Amurka a shirye suke su fara wata sabuwar tattaunawa.

Majiyoyin sun ce tattaunawar za ta kasance ba kai tsaye ba,  sanann kuma ana sa ran cewa kasar Norway ce za ta kasance mai shiga tsakanin bangarorin biyu.

Jaridar ta kasar Iran ta yi nuni da cewa “Tehran ta dage kan cewa batun biyan diyya a kan barnar da aka yi mata a yakin baya-bayan nan ya zama wani muhimmin bangare na duk wata tattaunawa a  nan gaba.”

A ranar  Alhamis kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta duk wata Magana kan wani takamaiman lokaci ko wurin da za a yi shawarwari da Washington, yana mai jaddada cewa “dukkan jita-jita game da hakan wani bangare ne na yakin tunani da kwakwalwa.”

Ya kara da cewa ofishin jakadancin kasar Switzerland yana aiki ne a matsayin cibiyar diflomasiyya tsakanin Tehran da Washington.

Amurka da Iran dai sun shafe kusan watanni biyu suna tattaunawa wadda ba ta kai tsaye ba, wanda Oman ke shiga tsakani, kafin Isra’ila ta kaddamar da farmakin tsokana a kan Iran a watan Yunin da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted