Iran Ta Yi Maraba Da Sulhuntawa Tsakanin Armenia Da Azerbaijan

Gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da sulhuntawa da kasashen Armedia da Azarbaijan a fadar white House, amma ta yi gargadin shishigin kasashen waje a

Gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da sulhuntawa da kasashen Armedia da Azarbaijan a fadar white House, amma ta yi gargadin shishigin kasashen waje a yankin Caucasus, da ke makobtaka da Iran.

Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta ta nakalto wani bayani wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a yau Asabar na cewa, sasantawa tasakanin kasashen biyu wani ci gaba wanda zai iya kaiwa ga tabbataccen zaman lafiya a yankin da kuma ci gaba ga dukkan kasashen yankin.

Amma a wani bangare kuma bayanin ya bayyana cewa akwai tsoron kasashen waje musamman Amurka tana iya amfani da wadannan kasashen don cutar da yankin ko wasu kasashe. Don haka ta yi kira ga wadannan kasashe biyu su yi hattara.

Kafin haka dai kasashen Azarbaija da Armenia sun shiga yake-yake sau da dama dangane da yankin n Karabakh wanda a yakinsu na karshe-karshen nan jumhuriyar Azarbaijan ta kwace shi daga hannun Armenia.

Sai dai gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa shirin samar da wani babban titi a yankin zangon kasa ne da tsaron kasar Iran. Ba don kom,e ba sai don Amurka ce take son samar da wannan titin.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted