Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta kafa kwamitin tsaron kasa, wanda zai kula da sabbin matsalolin tsaron kasa, da kuma da kuma karfin sojojin kasar .
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne tare da dogaro da duka da 176 da kundin tsarin mulkin kasar.
Labarin ya kara da cewa , kafa kwamitin wani mataki ne, na kyautata harkokin tsaron kasar, da kuma samar da mafita ga wasu sabbin matsalolin tsaro wadanda kasar take fuskanta. Da kuma tabbatar da cewa jami’an tsaron kasar a shirye suke su fuskanci duk wata barazanar tsaron da zasu bullowa kasar nan gaba.
Banda haka kwamitin shine zai shirye dabarbarin kare kasar tsakanin bangarori daban0daban na sojojin da jami;an tsaron kasar. Banda haka kwamitin ne da alhakin gano duk irin barazanar tsaron da kasar zata faskanta sannan ta dauki matakan da suka dace a lokacinda ya dace.