Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD

Firay minisatan kasar Canada Mark Corney ya bada sanarwan cewa gwamnatin kasarsa zata amince da samuwar kasar Falasdinu a babban taron MDD a cikin watan

Firay minisatan kasar Canada Mark Corney ya bada sanarwan cewa gwamnatin kasarsa zata amince da samuwar kasar Falasdinu a babban taron MDD a cikin watan satumba mai zuwa a birnin NewYork.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Carney yana fadar haka a yau Alhamis ya kuma kara da cewa gwamnatinsa ta dauki wannan matsayin ne, bayan abin bakin cikin da ke faruwa a Gaza, na amfani da yunwa a matsayin makami wanda HKI take yi. Sannan tare da matakan da gwamnatocin kasashen Faransa da Burtania suka dauki na yin haka a taron.

Kasar Canada, a baya dai , tana daga cikin kasashen yamma wadanda suke goyon bayan HKI ido rufe. Bayan fara yakin Tufanaul Aska a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 , gwamnatin kanada suna daga cikin gwamnatocin kasashen yamma wadanda suka bayyana cewa HKI tana kare kanta ne daga kungiyar Hamas.

A cikin watnni 4 da suka gabata HKI ta hana shigowar abinci da magunguna zuwan cikin gaza, wanda ya kai ga a cikin makonnin da suka gabata, bayan kashe mutane kimani 60,000 da makamai, yunwa kuma ta kashe kimani mutane 160 mafi yawansu jarirai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted