Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi kakkausar suka ga sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa kasarta Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i, ya

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi kakkausar suka ga sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa kasarta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane, hukumomin shari’a da jiragen ruwa masu alaka da makamashi da man fetur na Iran sabbin takunkumi.

Baqa’i ya gwada rashin amincewar Iran da bakar siyasar Amurka da na ‘yan sahayoniyya musamman farmakin da Amurka da gwamnatin sahayoniyya suka kaddamar na baya-bayan nan kan kasar Iran, yana mai bayyana kakaba takunkumin a matsayin baya da wani harumi na doka kawai matakin zalunci ne kan Iran lamarin da ke fayyace kiyayyar Amurka karara kan Iran.

Baqa’i ya kara da cewa: Al’ummar Iran suna sane da mummunar manufar wadannan tsauraran takunkumin da suke da nufin raunana Iran da neman take mata kowane irin hakki, za su tsaya da dukkan karfinsu wajen kalubalantarsu domin kare mutunci da muradunsu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada cewa: Dabi’ar da Amurka take gudanarwa na nuna son kai da kuma bin hanyar da ba ta dace ba da tilastawa wajen cimma haramtattun manufofinta a matakin kasa da kasa, da kuma rashin mutunta tsarin doka da ‘yancin bil Adama, sun yi hannun riga da tushen dokokin kasa da kasa, gami da ka’idar mutunta ‘yancin kasashe da ‘yancin cinikayya tsakanin kasashe, da kuma daukan matakan nuna barazana ga duniya da ba a taba gani ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted