Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa kyale HKI wanda kasashen duniya suka yi ne, ya ke bawa HKI karfin giwan

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa kyale HKI wanda kasashen duniya suka yi ne, ya ke bawa HKI karfin giwan ci gaba da abinda take yi a gaza.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun dokokin wanda ake gudanarwa a halin yanzu a birnin Geneva.

Wannan dai shi ne taron shuwagabannin majalusun dokoki na duniya karo na 6 wanda MDD take daukar nauyinta.

Dangane da hare-haren da HKI da Amurka suka kaiwa kasar Iran a cikin watan Yunin da ya gabata kuma ,Qalibof ya bayyana cewa manufarsu it ce lalata shirin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, kwata-kwata. Alhali hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA tana sanya iado a kan ayyukan sarrafa uranium da kasar take yi.

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa hare-haren kwanaki 12 wanda wadan nan kasashe biyu wadanda basa son zaman lafiya a Iran sun kai mutane kimani 1100 ga shahada. Sannan sun sanya shirin nukliyar kasar Iran cikin hatsari, wanda ya tilasta mana daukar matakai don kare shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted