Taron ‘Kasashen Faransa Da Saudiyya A Gefen Taron MDD A NewYork

A dai-dai lokacinda hankalin mutane da dama suka tashi dangane da abinda ke faruwa a Gaza, kasashen Faransa da saudia sun shirya gudanar da gagarumin

A dai-dai lokacinda hankalin mutane da dama suka tashi dangane da abinda ke faruwa a Gaza, kasashen Faransa da saudia sun shirya gudanar da gagarumin Taro a birnin New na kasar Amurka a dai-dai lokacinda ake gudanar da babban taron majalisar dinkin duniya na shekara-shekara.

Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Faisal Bin Farhan yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, za’a gudanar da taron a ranar 28-29 ga watan Yulin da muke ciki , kuma akwai fatan kasashen duniya zasu tattaunawa wannan batun sosai don kawo karshen rikicin gabas ta tsakiya bayan shekaru fiye da 70 ana gudanar da ita.

Ministan ya kara da cewa a wannan taro nana saran shugaban kasar Faransa Emmanuel Mocron zai shelanta amincewar kasar faransa da kasar Falasdinu mai zaman kanta a kan iyakoki na shekara 1967. Wato yankunan da MDD ta amince a matsayin iyakokin HKI da kuma na Falasdinawa.

Yankunan dai sun hada da Gaza da yankin yamma da kogin Jordan,

Sai dai a halin yanzu gwamnatin HKI ta samar da dokoki wadanda suka tabbatar da kwace dukkan wadannan yankunan daga hannun Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted